Tun daga kan shugaba ake fara yakar cin hanci da rashawa - Kagame

Tun daga kan shugaba ake fara yakar cin hanci da rashawa - Kagame

A yau Talata 11, ga watan Yuni, shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, ya ziyarci Najeriya domin halartar taron yaki da rashawa na ranar dimokuradiyar kasar nan da aka gudanar a babban birnin kasar nan na Tarayya.

Shugaban jamhuriyyar Rwanda Paul Kagame, ya ce ba bu ta yadda za ayi a cimma nasarar yaki da rashawa a nahiyyar Afirka da kuma ko ina a fadin duniya matukar dokar yaki da rashawa ba ta fara aiki tun daga kan shugabanni ba.

Mista Kagame ya ce annobar rashawa ta samu wurin zama tare da yin kane-kane a nahiyyar Afirka a sakamakon yadda ta samu karbuwa daga bangaren shugabanni da suka karbe ta hannu biyu-biyu.

Ya ce cimma nasarar a kan yaki da rashawa ba ta daukar wani lokaci mai tsawo illa iyaka muhimmanci na kyakkyawar aniya da shugabanni suka kulla na da tasiri gaske wajen gaggauta fatattakar annobar rashawa daga kowane yanki.

KARANTA KUMA: Abubuwa 5 game da sabon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, shugaban kasar Rwanda ya gabatar da wannan jawabai yayin halartar taron yaki da rashawa na ranar dimokuradiya wanda hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC ta dauki nauyin gudanar wa a garin Abuja.

Taron na yaki da rashawa ya samu halarcin shugaban kasa Buhari, kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu da kuma mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel