Zaben majalisa: Yadda Sanata Lawan, danlelen Buhari, ya kayar da Sanata Ndume, shalelen PDP

Zaben majalisa: Yadda Sanata Lawan, danlelen Buhari, ya kayar da Sanata Ndume, shalelen PDP

Sanata Ahmed Lawan, danlelen shugaban kasa da jam'iyyar APC a zaben shugaban majalisar dattijai, ya samu nasarar buga abokin hamayyarsa da jam'iyyar PDP ke mara wa baya, sanata Ali Ndume, da kasa a zaben da aka yi yau, Talata.

Lawan ya zama sabon shugaban majalisar dattijai bayan ya samu adadin kuri'u 79, yayin da abokin takararsa kuma shalelen jam'iyyar PDP, Sanata Ndume, ya samu kuri'u 28 kacal.

Sanatoci 107 da ke zauren majalisar dattijai ne suka kada kuri'un zaben wanda zai jagorance su. Majalisar na da jimillar mambobi 109 amma har yanzu hukumar zabe ba ta kammala warware matsalar Sanatoci biyu ba daga jihar Imo.

Sanata Yahaya Abdullahi, dan jam'iyyar APC daga jihar Kebbi, ne ya fara zaben Lawan a matsayin dan takara bayan rantsar da majalisar sannan Sanata Adeola Olamilekan, dan jam'iyyar APC daga jihar Legas, ya goya masa baya.

Ndume ya ki janye takararsa duk da jam'iyyar APC da fadar shugaban kasa sun fito fili sun bayyana goyon bayansu ga Lawan.

DUBA WANNAN: Abinda Sanata Ndume ya fada wa APC bayan Sanata Lawan ya kayar da shi

Sakamakon zaben ya nuna cewaer hatta mambobin jam'iyyar PDP a majalisar ta dattijai sun kada kuri'ar su ne ga Lawan.

A daren ranar Litinin ne jam'iyyar PDP ta kira wani taron gagga wa na zababbun sanatocin ta domin wargatsa shirin jam'iyyar APC da fadar shugaban kasa na son ganin Lawan ya zama shugaban majalisar dattijai.

Saidai, PDP ta makara wajen kiran taron zababbun Sanatocin domin majiyar Legit.ng ta shaida mata cewa da yawa daga cikin mambobin majalisar na jam'iyyar basu halarci taron ba.

Rashin halartar mambobin ba zai rasa nasaba da gum din da jam'iyyar PDP ta yi ba a kan zaben shugaban majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel