Amurka tayi kira ga sababbin shuwagabannin Majalisar Najeriya

Amurka tayi kira ga sababbin shuwagabannin Majalisar Najeriya

Mataimakiyar shugaban jakadancin Amurka na Najeriya, Kathleen FitzGibbon, tayi kira ga sababbin shuwagabannin majalisa da su taimaka wajen magance matsalolin tsaro a Najeriya.

FitzGibbon, daya daga cikin baki na musamman, wacce ta wakilci shugaban jakadancin, tayi kiran ne bayan da aka kaddamar da majalisar ta tara.

Ta kara da cewa, Majalisar tashiya yin aiki da wuri don a magance matsalolin tsaro, talauci da cigaban kasarnan.

"Muna fata majalisar zata fara aiki da wuri-wuri don magance wasu matsalolin kasarnan musamman matsalolin tsaro, ci gaba da dai sauransu."

"Na tabbata duk wanda yake wajennan bukatarsa kenan."

"Akwai bukatar su zabi shuwagabanni masu nagarta masu kishin al umma."

Ta kuma bukaci yan majalisar da su wakilci yankunansu don cika masu burikansu.

"A matsayinsu na wakilan al'umma, suna sane da bukatun al'ummarsu ina kuma fatan zasu cika masu bukatunsu."

Ta kara da cewa "muna fatan zamu ga canje canje masu kyau a wannan shekarar da kuma majalisar."

Karanta wannan: Buhari ya yi alhinin mutuwar Farfesa Layi Fagbenle

Daga karshe, FitzGibbon ta bukaci yan Najeriya dasu yi ma shuwagabanninsu zato na gari da kuma addu'a don tafiyar da kasar nan gaba

Tace "kamar yadda yan Najeriya suke fatan alheri, su cigaba da fatan alherin kuma su taimaka ma shuwagabanninsu don tafiyar da kasarsu gaba da kuma magance matsalolin tsaro."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel