Abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege

Abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege

Obarisi Ovie Omo-Agege ya kasance lauyan Najeriya kuma dan siyasa. Sanata ne mai wakiltan mazabar jihar Delta ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya na takwas.

Omo-Agege ya kasance dan asalin Orogun dake karamar hukumar Arewacin Ugheli a jihar Delta. Yayi nasarar zama mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya a ranar 11 ga watan Yuli, 2019 bayan ya doke dan adawansa da tazarar kuri’u 31 inda ya lashe matsayin mataimakin shugaban majalisan dokoki na kasa.

1. Takaitaccen tarihin rayuwarsa

An haifi Omo-Agege a ranar 3 ga watan Agusta, 1963 a jihar Delta. Ya halarci makarantan Firamare na St. George Grammar school, Obinomba Obiaruku a jihar Delta.

2. Matakin karatunsa

Omo-Agege ya kammala karatunsa na digiri daga jami’an Benin a 1985 inda ya karanci shari’a. Ya zama cikakken lauya a 1986.

A 2002, ya kammala digiri na biyu a shari’a a jami’ar Tulane University Law School.

3. Aiki

An tura Omo-Agege zuwa jihar Kwara don bautar kasa Ya kammala NYSC a cibiyar bincikenmasu laifi na rundunar yan sandan Najeriya. Omo-Agege ya soma aikin shari’a tare da PAT OKUPA & Co in a Lagas a 1987.

A 1989, Omo-Agege ya koma Legas sannan ya kafa cibiyar shari’a; Agege & Co. Omo-Agege ya koma Amurka a 1990, inda yayi aiki a matsayin wakilin kasar waje a ofishin Charles O Agege's law a Los Angeles, Califonia.

Omo-Agege ya dawo Najeriya a 1992 don kafa Omo-Agege & Associates inda har ila yau ya kasance babban abokin tarayya. A 1996 ya hada kamfanin shi mai suna Omo-Agege & associates da wani kungiya inda sunansa ya sauya zuwa Agege & Esin.

4. Rayuwar siyasarsa

Omo-Agege ya shiga fagen siyasa inda ya tsaya takaran tikitin kujerar dan majalisa a majalisan dokokin jihar Delta a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), inda ya fadi a zaben fidda gwani na jam’iyyar. A 2003, tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, ya nada Omo-Agege a matsayin kwamishinan ayyuka na musamman.

Omo-Agege ya tsaya takaran kujerar Gwamnan jihar Delta amman bai yi nasara ba a zaben fidda gwani na jam’iyyar People Democratic Party's inda Gwamna Emmanuel Uduaghan yayi nasara.

Gwamna James Ibori ya nada Omo-Agege a 2007 a matsayin Sakataren gwamnatin jihar.

KU KARANA KUMA: Yadda zaben kakakin majalisar wakilai ke gudana

Omo-Agege ya tsaya takaran Majalisan dattawa a 2015 a karkashin jam’iyyar Labour Party. An zabe shi a matsayin dan majalisa mai wakiltan yankin Delta ta tsakiya a ranar 28 ga watan Maris, 2015.

Omo-Agege ya sauya sheka daga Labour Party zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a ranar 7 ga watan Maris, 2017.

Ovie Omo-Agege ya kasance sanata mai wakiltan yankin Delta ta tsakiya a zaben 2019.

A 2019, ya lashe zaben majalisar dattawa ta tara inda yayi nasaran zama sabon Mataimakin Shugaban Majalisan Dattawa bayan ya samu kuri’u 68 inda ya doke Ike Ekweremadu da kimanin tazaran kuri’u 37.

5. Rayuwar iyalinsa

Omo-Agege na da aure da kuma yara biyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel