JAMB, jami'oi sun kayyade 160 a matsayin mafi karancin makin shiga jami'a

JAMB, jami'oi sun kayyade 160 a matsayin mafi karancin makin shiga jami'a

- Idan kana son shiga jami'a a wannan shekarar, sai ka samu maki 160

- An kara maki 40 kan na shekarar baya wanda yake 120

Kamar yadda ya fara a shekarun baya, Hukumar gudanar da jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare wato JAMB, karkashin jagorancin farfesa Ishaq Oloyede, ta sake zama domin tattaunawa kan mafi karancin makin wannan shekara.

A taron tsara hanyoyin shiga makarantun gaba da sakandare na 19, an amince da 160 a matsayin maki mafi karanci don samun gurbin karatu a jami'oin gwamnati na 2019.

Taron wanda ya gudana a dakin taro na Bola Babalakin, jihar Osun, a ranar Talata 11 Yuni, 2019, an kuma amince da 140 a mtsayin maki mafi karanci don shiga jami'oi masu zaman kansu.

KARANTA KUMA: Kotu ta umurci ayi yar tinke a zaben Majalisar tarayya

Haka zalika, an amince da 120 don shiga makarantun polytechnic na gwamnati, sa'annan 110 don shiga makarantun poly masu zaman kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel