Takarar shugabancin majalisa: Dalilai 5 da suka sa Lawan ya kayar da Ndume

Takarar shugabancin majalisa: Dalilai 5 da suka sa Lawan ya kayar da Ndume

A ranar Talata 11 ga watan Yunin 2019 ne Sanata Ahmad Lawan na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya zama shugaban majalisar dattawa ta 9.

Lawan ya yi nasarar zama shugaban majalisar ne bayan ya kayar da Sanata Ali Ndume da kuri'u 79 da 28. Ga wasu dalilai da suka sanya Lawan ya kayar da Ndume:

1 - Samun goyon bayan jam'iyyar APC

Kwamitin Gudanarwa (NWC) na APC ta gana da gwamnoni da zababun 'yan majalisa na jam'iyyar a ranar Litinin a Abuja inda suka amince kan wanda za su zaba a matsayin shugaban majalisar dattawa, Kakakin majalisar wakilai da mataimakansu.

Mahallarta taron sun zabi Ahmad Lawan a matsayin shugaba saboda haka ana iya cewa goyon bayan da ya samu daga APC yana daga cikin dalilan da ya sa ya yi nasara.

2 - Sa bakin Shugaba Buhari

A ranar 6 ga watan Yuni, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi taro da Danjuma Goje da Ahmed Lawan. Bayan taron, Goje ya janye daga takarar wanda hakan alama ce da ke nuna Lawan ne zabin Buhari.

DUBA WANNAN: Har yanzu Ganduje da Sanusi ba su yi sulhu ba - Hadimin Gwamna

3 - Rashin karbuwa da Ndume bai samu ba

Galibin sanatocin jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) ba su zabi Ndume ba duk da cewa kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta goyi bayansa.

Mafi yawancin su ba su gamsu da Ndume ba duk da cewa shekarun baya ya kasance cikin jam'iyyar ta PDP amma daga baya ya fice. Babu mamaki hakan ya sa ba su amince da shi ba.

4 - Rashin daukan matakin kan lokaci da PDP ba ta yi ba

Jam'iyyar PDP ba ta bayyana goyon bayan ta ga Ndume ba sai a safiyar ranar Talata, sa'o'i kadan gabanin zaben na shugaban majalisar dattawa. Sanatoci da dama suna ganin anyi jinkirin daukan matakin. Idan da jam'iyyar ta bayyana ra'ayin ta kan Ndume da wuri, akwai yiwuwar ya yi nasara.

5 - Tuntubar mutane da yawa

Jam'iyyar APC ta goyi bayan Lawan a 2015 amma bai fita ya yi takara sosai ba. Ya yi tsamanin cewar jam'iyyar za ta yi masa komai amma wannan karon ya mike tsaye ya yi ta neman goyon bayan sanatoci duk da cewa APC ta goyi bayansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel