Yadda zaben kakakin majalisar wakilai ke gudana

Yadda zaben kakakin majalisar wakilai ke gudana

A majalisar wakilai inda mambobin majalisar ke gudanar da zamansu na farko a majalisa ta tara, a yanzu haka zukata na cike zilama, fargaba da kuma zuba idanu don ganin rawar ganin da magoya bayan manyan yan takarar kujerar kakakin majalisar za su taka.

Makonni da dama kafin bikin rantsarwar, yan takarar wadada suka hada da Femi Gbajabiamila, Emeka Nwajiuba da kuma Umaru Bago sun ziyarci jihohi fadin kasar inda suke ta tattaunawa da sarakunan gargajiya, gwamnoni dashugabannin siyasa domin neman kuri’u.

Kamfen din ya ba yan takarar damar bayyana manufofinsu gabannin zaben.

Yayinda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da bangaren zartarwa ke goyon bayan Gbajabiamila, wasu yan Najeriya na ganin fitowar Emeka Nwajiuba zai kawo hadin kai da kasar ke matukar bukata.

A yanzu haka an fara kada kuri’a tsakanin yan takara biyu, Gbajabiamila da Umar Bago, dukkaninsu yan APC ne.

Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya lashe zaben kakakin majalisar wakilan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Gaskiyar dalilin da yasa nayi takara da Omo-Agege - Ekweremadu

Gbajabiamila, wanda ke wakiltar mazabar ‎Surulere a jihar Legas, ya doke Umaru Bago daga jihar Niger.

Gbajabiamila ya samu kuri'u 281 yayin da Umar ya samu kuri'u 76.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel