Ranar Dimokuradiyya: Jihar Kebbi ta yi gayyata ta musamman ciki hadda tsoffin gwamnonin jihar

Ranar Dimokuradiyya: Jihar Kebbi ta yi gayyata ta musamman ciki hadda tsoffin gwamnonin jihar

- Gwamnatin jihar Kebbi ta shirya gudanar gagarumin biki domin murnar Ranar Dimokuradiyya wanda zai kasance a ranar Laraba 12 ga watan Yuni, 2019.

- Sani Dododo, sakataren yada labarai na APC jihar Kebbi shi ne ya bada wannan sanarwa ga manema labarai jiya Talata a Birnin Kebbi.

Gwamnatin Kebbi ta bayyana cewa ta gayyaci mutane 600 ‘yan asalin jihar wadanda suka hada da tsoffin gwamnonin jihar tun lokacin mulkin soja da kuma na farar hula, domin su halarci bikin Ranar Dimokuradiyya a ranar Laraba 12 ga watan Yuni a filin wasa na Haliru Abdu dake Birnin Kebbi.

Sakataren yada labarai na jam’iyar APC a jihar kuma shugaban hukumar samar da taimakon gaggawa wato SEMA, Alhaji Sani Dododo ne ya sanar da manema labarai ranar Talata a Birnin Kebbi.

KU KARANTA:'Yan bindiga sun sace dalibin shekarar karshe a jami'ar UDUS, Sokoto

Ya ce: “ A halin yanzu duk wani shiri domin gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali an riga da an kammala shi. Bikin zai kayatar matuka saboda akwai faretin jami’an tsaro da kuma baje fasahar al’adun gargajiya da za’a gabatar a wurin.”

“ Kamar yadda kuka sani shugaban kasa ya sanya 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Dimokuradiyya, wannan dalilin ne ya sanya ba za’a bar Kebbi a baya ba wurin murna da biki a wannan rana. Mun gayyaci mutane 600 ‘yan asalin jihar Kebbi cikinsu akwai tsoffin gwamnonin jihar nan tun mulkin soja.” Inji sakataren.

Dododo ya cigaba da cewa: “ Gwamna Atiku Bagudu zai kasance a Abuja domin taya shugaban kasa murnar wannan rana, a yayin da mataimakin gwamnan jihar Kebbi Alhaji Samaila Yombe zai karbi bakuncin manyan baki a madadin gwamnan a jihar.

Haka zalika, ya sake yin kira ga dukkanin al’ummar Kebbi, magoya bayan jam’iyar APC da kuma masu yiwa gwamnatinsu fatan alheri da su halarci taron.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel