'Yan bindiga sun sace dalibin shekarar karshe a jami'ar UDUS, Sokoto

'Yan bindiga sun sace dalibin shekarar karshe a jami'ar UDUS, Sokoto

Wasu 'yan bindiga sun sace Aliyu Maidamma, dalibin da ke shekararsa ta karshe a bangaren karatun 'Microbiology' ' a jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto a yayin da ya rage saura 'yan kwanaki kalilan a fara jarrabawar karshen kammala rabin zagayen zango.

Jaridar The Nation ta rawaito cewar 'yan bindigar sun far wa Aliyu ne ranar Juma'a yayin da yake hanyarsa ta koma wa Sokoto bayan kammala hutun Sallah karama.

A wata gana wa ta wayar tarho da jaridar ta yi da Ibrahim Sanni Maidamma, dan uwa ga Aliyu, ya tabbatar da sace dan uwan nasa ga The Nation.

A cewarsa: "a magana ta karshe da muka yi ranar Juma'a, Aliyu ya fada min cewar ya na kan hanyarsa ta komawa makaranta.

"Amma da misalin karfe 3:00 na rana da na kira shi ban same shi ba, na dauka matsalar network ce kafin daga bisani 'yan bindigar da suka sace shi su kira babban yayanmu tare da sanar da shi cewar sun kama Aliyu.

DUBA WANNAN: Yakubu Danladi, wani matashi mai shekaru 34, ya zama kakakin majalisar dokoki a jihar Arewa

"Da farko sun nemi a biya su miliyan N3 kafin su sake shi. Daga baya sun kara kira tare da yin gargadin cewar idan ba mu biya kudin ba zasu kashe shi.

"Mu na iya bakin kokarinmu domin ganin sun sake shi. Babban yayan mu na cigaba da magana da 'yan bindigar," Sani ya fada cikin murya mai rauni.

Shugaban kungiyar daliban jami'ar, Kwamred Faruk Barde, ya tabbatar da labarin sace Aliyu tare da bayyana cewar kungiyar daliban ba ta gana da iyayen Aliyu ba domin samun karin bayani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel