Shikenan: Bayan shekaru 6, Kotu ta wanke Amina Dauda daga zargin kisan maigidanta

Shikenan: Bayan shekaru 6, Kotu ta wanke Amina Dauda daga zargin kisan maigidanta

Wata babbar kotun birnin tarayya dake unguwar Maitama, birnin tarayya Abuja ta wanke wata matar aure, Amina Dauda, daga zargin kisan maigidanta, Mohammed Matazu, wanda ya kasance ma'aikacin gidan rediyon gwamnatin Najeriya, FRCN kafin rasuwarsa.

Amina Dauda, wacce aka gurfanar a ranar 22 ga watan Mayu, 2013 gaban alkali Hussein Baba-Yusuf kan laifin kisan kai yayinda yan sanda suka bukaci a yanke mata haddin kisa.

Yan sanda sun yi zargin cewa Amina ta watsawa mijinta man fetur kuma ta banka masa wuta a gidansu dake unguwar Gwarinpa dake garin Abuja.

Amma a ranar Juma'a, mai shari'a Baba-Yusuf, ya yanke cewa yan sanda basu gudanar da bincike mai zurfi ba kuma basu nuna kwarewa ba.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: INEC ta bukaci kotun zabe tayi watsi da karar Atiku da PDP

Yace: "Basu nuna kwarewa ba wajen gudanar da bincikensu, abinda suka kawai shine daukan jawabin matar da ziyartar gidan kuma basu samu wani hujja ba."

Alkali Baba-Yusuf ya kara da cewa duk da cewa an akwai hujja kisan gaban kotun, babu mai bada shaidan da yan sanda suka gabatar da ya kawo hujjan takamamman abinda ya faru.

Bai tsaya nan ba, ya ce dubi ga irin jawabin tilastawan da aka sanya Amina yi, ya nuna cewa bata aikata laifin da ake zarginta da shi ba.

Ya caccaki jami'in dan sanda mai bincike wanda ke da hakkin gudanar da bincike kan lamarin kan rashin sanin ya kamata wajen duba ingancin jawabin da Amina Dauda tayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel