Madalla: Abdurazak Isa na gina matatar man fetur akan kudi N7bn

Madalla: Abdurazak Isa na gina matatar man fetur akan kudi N7bn

Abdurazak Isa na daya daga cikin kalilan yan Najeria dake amfani da kudin aljihunsu don ganin an samu cigaba a bangaren samar da tataccen man fetur a Najeriya.

A cewar @ovieali akan shafin tiwita, Isa ya zuba zunzurutun kudi Naira biliyan 7 wajen gina matsakaiciyar matatar man fetur wanda zata taimaki Najeriya wajen samar da isasshen man fetur ba tare da an shigo dashi daga kasashen waje ba da kuma samar da ayyukan yi.

Shafin na tiwita ya kara da cewa, aikin matatar ya kusa kammaluwa kuma hakan zai sauya dogaron da Najeriya ke yi da kasashen waje don samar da tataccen man fetur.

A cikin watan Oktoba 2018, Abdurazak Isa ya zuba kudi Naira biliyan 7 don gina matatar man fetur din da niyyar samar da aikin yi sannan kuma ya magance matsalar man fetur a Imo da anambra ta hanyar samar da lita 271 a kowacce shekara.

Karanta wannan: Yadda zaben majalisar dokokin tarayya ke gudana

Ana hakan ne, Legit ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar yakubu Gawon(rtd), ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gina matatun man fetur a Portharcourt, Warri da Kaduna don samar da isasshen man fetur na amfanin cikin gida.

A yayin da yake magana a taron kungiyar horar da tallata man fetur ta duniya (OGTAN) a legas ranar Litinin 15, Afirilu 2019, tsohon shugaban kasan ya kara da cewa, gwamnatin sa tayi niyyar kara wasu matatun don fitar da tataccen man fetur ta yadda ba sai an dogara da wasu kasashen waje ba.

Legit.ng ta kuma ruwaito a ranar Alhamis, 25 Afirilu, babban daraktan hukumar samar da man fetur ta kasa (NNPC), Maikanti Baru, yana cewa, matatar man fetur da Aliko Dangote ke ginawa a legas itace jigo wajen tabbatar da samar da isasshen man fetur a kasar nan.

Shugaban na NNPC, ya ce idan aka gama gina matatar, zata rika fitar da gangar mai kimanin 650,000 a kowacce rana, wanda hakan zai rubanya abinda ake fitarwa yanzu a najeriya.

Najeria, wacce itace kasar da tafi kowace kasa tsotso danyen man fetur a Afirika, ta kasance tana shigowa da tataccen man fetur daga kasashen ketare shekara da shekaru.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel