Buhari da APC sun nemi kotun zabe ta soke karar da Atiku ya shigar

Buhari da APC sun nemi kotun zabe ta soke karar da Atiku ya shigar

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta shugaban kasa Muhammadu Buhari sun bukaci kotun zabe da ta kori karar da dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar da jam'iyyarsa suka shigar akan zaben shugaban kasa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Talata, 11 ga watan Yuni ya roki kotun zaben Shugaban kasa da ta soke karar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta na Shugaban kasa, Atiku Abubakar suka shigar da ke kalubalantar nasarar zabensa a karo na biyu.

Da farko Legit.ng ta rahoto cewa Jam'iyyar 'Coalition 4 Change' (C4C) da dan takarar ta na shugaban kasa a zaben da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabrairun 2019 sun janye karar da suka shigar na kalubalantar sakamakon zaben ya bayyana shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya sake samun nasara.

C4C da dan takarar ta sun janye karar ne daga kotun sauraron korafe-korafe a kan zaben shugaba kasa a ranar Litinin.

Kotun ta kori karar da jam'iyyar C4C da dan takarar ta, Geff Ojinika, suka shigar bayan sun mika takardar neman hakan. A takardar su da suka shigar da kara, mai adireshi CA/PEPC/003/2019, sun roki kotun da ta soke zaben shugaban da ya samar da shugaba Buhari a matsayin wanda ya yi nasara bisa zargin cewar zaben cike yake da saba dokokin zabe da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2010.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Yadda zaben mataimakin shugaban majalisar dattawa ke gudana

Jastis Mohammed Garba, sabon alkalin dake sauraron korafe-korafe a kan zaben shugaban kasa, ya amince da bukatar C4C da dan takarar ta na korar karar da suka shigar kammar yadda suka nema ta bakin lauyansu, Mista Obed Agu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel