Yanzu-yanzu: INEC ta bukaci kotun zabe tayi watsi da karar Atiku da PDP

Yanzu-yanzu: INEC ta bukaci kotun zabe tayi watsi da karar Atiku da PDP

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta bukaci kotun zabe tayi watsi da karar da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta. Atiku Abubakar, suka shigar kan nasarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Jam'iyyar PDP da Atiku Abubakar suna kalubalantar sanar da shugaba Buhari a matsayin zakaran zaben shugaban kasan 23 ga watan Febrairun 2019.

A wata bukata da hukumar INEC ta shigar ta bakin lauyanta Hustaz Usman, INEC ta bukaci kotun zabe tayi fatali da bukatar PDP akan rashin ambatar sunan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, cikin karar da ta shigar.

Kana Hustaz Usman ya shigar da wasu bukatu hudu daban-daban domin kokarin gamsar da kotun kanwatsi da PDP.

KU KARANTA: Kotu ta umurci ayi yar tinke a zaben Majalisar tarayya

Amma lauyan PDP, Levi Uzoukwu, ya siffanta wannan bukata na APC a matsayin wani bakon abu a hakokin kotu kuma ya bukaci kotun ta yi watsi da bukatar.

Bayan sauraron kararsu, shugaban kotun, Mohammad Garba, ya dakatad da zaman kuma ya ce zai sanar da ranar dawowa daga baya.

Mohammed Garba ne sabon babban alkalin kotun bayan janyewar shugabar kotun daukaka kara, Zainab Bulkachuwa, a makonnin baya.

A ranar Litinin, daya daga cikin jam'iyyun siyasa hudu da suka shigar da kara kotun kara, jam'iyyar Congress 4 Change C4C, ta yanye kararta kuma ta amince da Buhari matsayin wanda yayi nasara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel