Yakubu Danladi, wani matashi mai shekaru 34, ya zama kakakin majalisar dokoki

Yakubu Danladi, wani matashi mai shekaru 34, ya zama kakakin majalisar dokoki

Yakubu Saliu Danladi, matashi mai shekaru 34, ya zamam shugaban majalisar dokokin jihar Kwara.

Wannan shine karo na farko da Danladi ya fara zuwa majalisar dokokin bayan ya lashe zabe a karkashin inuwar jam'iyyar APC daga mazabar Ilesha-Gwanara.

Honarabul Saheed Popoola, mamba a majlisar daga mazabar Balogun-Ojomu da ke karamar hukumar Offa, ne ya fara bayyana sunan Danladi a matsayin wanda zai jagoranci majalisar kafin daga bisani ya samu goyon bayan abokinsa honarabul Haliru Danbaba.

Da ya ke karbar mukamin shugabancin majalisar, Danladi ya bayyana cewar ya sadaukar da kansa domin hidinmta wa majalisar da jihar Kwara.

DUBA WANNAN: Bata ruwa: Gwamnan PDP da Sanatocin jam'iyyar sun shiga ganawa a gaggau ce

Da yake gabatar da shi a gaban ragowar mambobin majalisar, Popoola ya ce an haifi Danladi, mamba daga mazabar Ilesha/Gwanara a karamar hukumar Baruten, a ranar 31 ga watan Mayu na shekarar 1985 a garin Gwanara.

Ya yi karatun makarantar Firamare a Gwanara daga shekarar 1988 zuwa 1993, daga nan ya tafi makarantar Sakandire ta St Anthony dake garin Ilorin, wacce ya kamma a shekarar 2001.

Ya yi karatun difloma da babbar difloma a bangaren injiniyarin a kwalejin kimiyya ta kasa da ke garin Kaduna (KADPOLY) daga shekarar 2003 zuwa 2008.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel