San barka: Dagaci ya bada fadarsa a dinga karbar haihuwa da duba marasa lafiya a Kaduna

San barka: Dagaci ya bada fadarsa a dinga karbar haihuwa da duba marasa lafiya a Kaduna

- Wani Dagaci mai kishin jama'arsa ya bayar da fadarsa a dinga karbar haihuwa da duba marasa lafiya

- Ya ce tausayin jama'ar tasa ne yasa ya bada fadar tasa, inda sai sun yi tafiyar kilomita 20 kafin su je asibiti domin duba lafiyarsu

Wani abin tausayi da ya faru a kauyen Kangimi-Ubangida dake cikin karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna, inda Dagacin kauyen ya bayar da fadarsa da yake mulki aka mai da ita asibiti, inda ake karbar marasa lafiya da mata masu haihuwa.

Dagacin kauyen mai suna Abdullahi Ubangida ya bayyana cewa yayi hakan ne bayan ya lura cewa mutanen kauyen sai sunyi tafiya ta kilomita 20 kafin su je asibitin unguwar Kawo na cikin garin Kaduna, wanda shine yafi kusa da su. Sannan wasu kuma sukan je asibitin Maraban Jos.

KU KARANTA: Kakakin majalisar Kano: Dan takarar gwamnati ya sha kaye

"Saboda rashin asibiti a kusa damu yasa muke asarar mata da yara a lokuta da dama.

"Ganin hakan na neman fin karfinmu, sai na shiga cikin gari nayi magana da malaman asibiti da su dinga zuwa garinmu suna duba marasa lafiya.

"Hakan yasa duk ranar Talata zan shiga cikin garin Kaduna na siyo magunguna wanda malaman asibitin za su yi amfani dasu idan sun zo. Hakan ya sanya dole na hakura da fada ta na bai wa malaman asibitin domin su dinga duba marasa lafiyan tunda ba mu da asibiti a kauyen.

"Abu na biyu da muke bukata bayan asibiti shine dakin ajiye magani. Saboda shi ma yana daya daga cikin matsalolin da muke fama da ita a kauyen mu," in ji Dagacin.

Akalla mutanen kauyen Kangimi-ubangida sun kai kimanin mutane 40,000, sannan a cewar Dagacin kauyen ya kai kimanin shekaru 200 da kafata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel