Kakakin majalisar Kano: Dan takarar gwamnati ya sha kaye

Kakakin majalisar Kano: Dan takarar gwamnati ya sha kaye

- Dan takarar jam'iyyar PDP ya lashe zaben kujerar Kakakin majalisar jihar Kano

- Inda ya samu kuri'u 21, yayin da dan takarar jam'iyyar APC wanda shi gwamnatin jihar ke goyawa baya ya sha kaye, bayan ya samu kuri'u 18

Mambobin majalisar dokokin jihar Kano sun zabi Abdul'aziz Gafasa a matsayin sabon Kakakin majalisar jihar a karo na tara.

Zaben ya biyo bayan sanar da fitowa takararsa da dan majalisar jam'iyyar PDP mai wakiltar karamar hukumar Dala, Lawan Hussain yayi jiya Litinin a lokacin da suka gabatar da zaman farko a dakin majalisar.

Gafasa ya taba shugabantar majalisar jihar a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau, a yanzu ya samu goyon bayan dukkanin mambobin jam'iyyar PDP su goma sha uku dake majalisar jihar.

Bayan haka kuma ya samu goyon bayan wasu mambobin jam'iyyar APC guda 8.

KU KARANTA: Rayuwa bayan mutuwa: Wata budurwa ta bayyana yadda ta dawo duniya bayan kwanaki da mutuwar ta

Majiya mai karfi ta bayyanawa jaridar Premium Times cewa, sauran mambobin jam'iyyar APC guda 18 sun zabi dan majalisa mai wakilatar karamar hukumar Doguwa.

Hakan ya bai wa Gafasa damar samun kuri'u 21, yayin da shi kuma dan majalisa mai wakiltar Doguwa, wanda aka tabbatar da cewa shi gwamnatin jihar ke goyon baya ya samu kuri'u 18.

Haka kuma an zabi dan majalisa mai wakilatar karamar hukumar Makoda, Hamisu Cigari, a matsayin mataimakin Kakakin majalisa a karo na hudu.

Gafasa ya nuna farin cikinsa ga 'yan majalisar da zaben shi da suka yi, sannan kuma yayi alkawarin ba zai watsa musu kasa a ido ba.

Ya kuma sha alwashin yin aiki da kowanne mamba na majalisar duk da cewa suna da bambancin jam'iyya da wasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel