Kai tsaye: Yadda zaben mataimakin shugaban majalisar dattawa ke gudana

Kai tsaye: Yadda zaben mataimakin shugaban majalisar dattawa ke gudana

Sanata Omo-Agege na da kuri’u 68, yayinda Sanata Ekweremadu na PDP ked a 37, sanata daya bai yi zabe ba, sannan an samu kuri’a mara kyau guda daya.

Sanata Omo-Agege ne kan gaba yayinda aka fara kirga kuri'un zaben mataimakin shugaban majalisar dattawa.

An kammala shiri tsaf domin fara zaben wanda zai zamo mataimakin shugaban majalisar dattawa na tara.

Zababben sanatan Katsina ta arewa Ahmad Babba- Kaita ya gabatar da sanata Ovie Omo-Agege a matsayin dan takarar mataimakin Shugaban majalisar dattawa.

Zababben sanata mai wakiltan Enugu ta arewa, ya gabatar da tsohon mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ga matsayin da ya bari.

Sanata Ekweremadu ya zagi Omo Agege a zauren majalisar dattawa, ya tuna lamarin sace sandar iko a majalisar dattawa ta takwas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel