Buhari ya yi alhinin mutuwar Farfesa Layi Fagbenle

Buhari ya yi alhinin mutuwar Farfesa Layi Fagbenle

Da ya ke dai Hausawa na yi ma ta kirari da mutuwa rigar kowa, mun samu cewa an yi babban rashi a kasar nan ta Najeriya yayin da wani zakakurin malamin kimiyya da fasaha, Farfesa Richard Olayiwola Fagbenle ya riga mu gidan gaskiya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar Farfesa Fagbenle tare da jajantawa da kuma bayar da hakurin rashi ga iyalai, 'yan uwa, makusanta, da kuma abokanan huldar sa.

Farfesa Fagbenle wanda ya bar duniya yana da shekaru 79, ya kasance fitaccen masanin ilimin fasaha a fannin nazarin Mechanical Engineering da babu shakka ya zamto abun alfahari ga Najeriya a kasashen duniya daban daban.

Marigayi Fagbenle a shekaar 1990 ya kasance babban ma'aikacin majalisar dinkin duniya yayin da ya rike wasu madafan iko a ma'aikatun fasaha na kasar Bostwana da kuma Afirka ta Yamma na tsawon shekaru hudu.

Shugaban kasa Buhari cikin sanarwar sa ta alhini da sanadin mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya ce Marigayi Fagbenle yayi rayuwar sa ya kasance madubin dubawa a fagen ilimi da ya yi fice inda yake masa fatan mutuwar sa ta zamto hutu a gare shi.

KARANTA KUMA: Zaben shugabanni: Gwamnonin APC sun mamaye majalisar Tarayya

Shugaba Buhari ya hori malaman ilimi a kan koyi tare da bibiyar sahun Marigayi Fagbenle domin cin moriyar kasar nan da kuma al'ummar duniya baki daya.

Ya kuma roki Mai Duka da ya kyautata makwancin Marigayi Fagbenle wanda a cewar sa ba za a taba mantawa da shi ba kasancewar sa shugaba na farko a wasu cibiyoyin ilimi uku daban daban na kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel