Babu wanda ya sanyamu mu binciki Sarki Sanusi - Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano

Babu wanda ya sanyamu mu binciki Sarki Sanusi - Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano

- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa na jihar Kano tace babu wanda ya sanya ta binciken Sarki Sanusi

- Shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimingado hukumar tana aiki ne akan rubutacciyar kara da korafe-korafe da ta samu daga al’umma bisa zargin masarautar da almubazaranci

- Ya kara da cewa hukumar tana gudanar da aikinta ne da kanta bisa yanda sashi na 8,9 da 15 na dokar hukumar yaki da cin hanci da rashawa na 2008 ta tanadar

Shugaban hukumar jin korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa na jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado a ranar Litinin ya bayyana cewa babu wanda ya tunzura hukumar da ta binciki harkokin kashe-kashen kudaden masarautar jihar.

Rimingado, wanda yayi magana da manema labarai a ofishinsa, yace hukumar bata hada lamarinta da kowa ba a wajen binciken da take gudanarwa kan masarautar bisa zargin kashe kudade ba bisa ka’ida ba.

Ya kara da cewa hukumar tana gudanar da aikinta ne da kanta bisa yanda sashi na 8,9 da 15 na dokar hukumar yaki da cin hanci da rashawa na 2008 ta tanadar.

A cewar shi, hukumar tana aiki ne akan rubutacciyar kara da korafe-korafe da ta samu daga al’umma bisa zargin kashe kudade ba a hanyar da ta dace ba a masarautar Kano a karkashin Sarki Muhammadu Sanusi II.

KU KARANTA KUMA: Ndume da Bago basu halarci ganawar da shugaba Buhari yayi da yan majalisan APC ba

Yace “An soma gudanar da wannan binciken ne tare da umurnin gwamnatin jihar Kano, amman bisa sakamakon ganin yanda al’umman jihanr ke korafi.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel