Kada ma ka fara! Uwargidar Sanata Shehu Sani ta gargade shi akan kyautar da kudin sallamarsa

Kada ma ka fara! Uwargidar Sanata Shehu Sani ta gargade shi akan kyautar da kudin sallamarsa

- Uwargidar Sanata Shehu Sani ta gargadi maigidan nata akan kyautar da kudin sallamarsa

- Tsohon Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a ranar Lahadi ya sadaukar da kudin alawus dinsa ga iyalan Leah Sharibu

- Tsohon dan majalisar yace matarsa tace kada ma yyi yunkurin sadakar da alawus dinsa kamar yadda Saraki yayi

Uwargidar tsoon sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokoki na takwas, Sanata Shehu Sani ta gargadi mijin nara akan sadakar da alawus dinsa da zai samu ga yan gudun hijira da sauran mutanen da kashe-kashen arewacin kasar ya shafa.

Legit.ng ta rahoto cewa sanatan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 10 ga watan Yuni, a shafinsa na twitter, cewa martain matarsa tace kada yayi yunkurin sadakar da kowani bangare na alawus dinsa.

Yace a lokacin da ya gabatar masa da wani sako game da yadda Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya sadaukar da nasa alawus din ga iyalan Leah Sharibu da yan gudun hijira, sai tayi kamar bata karanta ba.

Sanata Sani ya bayyana cewa hakan yasa ya kara tura mata sakon, amma sai matarsa ta amsa da kada ya yi kokarin aikata hakan.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Yadda zaben majalisar dokokin tarayya ke gudana

Ya wallafa a shafinsa na twitter: “A jiya, na gabatar da sakon Intagram ga matata cewa Shugaban majalisar dattawarmu mai barin gado ya sadaukar da alawus dinsa ga iyalan Leah Sharibu da yan gudun hijira, da farko tayi kamar bata karanta ba, bayan na sake tura mata sai ta amsa da: ‘Na san ka sosai, kada ma ka gwada yin hakan.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel