Zaben shugabanni: Gwamnonin APC sun mamaye majalisar Tarayya

Zaben shugabanni: Gwamnonin APC sun mamaye majalisar Tarayya

A yayin da a yau Talata 11, ga watan Yuni, za a rantsar da 'yan majalisa karo na tara a tarihin dimokuradiyyar kasar nan, gwamnonin jam'iyya mai ci ta APC sun mamaye zauren majalisar Tarayya dake babban birnin kasar nan na Abuja.

Bisa jagorancin gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi, tawagar gwamnonin APC kai tsaye ta afka zauren majalisar dattawan kasar nan kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Mashahurai cikin tawagar gwamnonin sun hadar da Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak; gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da kuma gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina.

Sauran 'yan tawagar sun hadar da gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalung, Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi da kuma gwamnan jihar Osun, Adeboyega Oyetola.

KARANTA KUMA: 2019: Cikin tsanani na rikicin zabe Buhari ya samu nasara - HRW

Kazalika tawagar ta kuma hadar da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari tare da takwaran sa na jihar Borno, Kashim Shettima.

Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin da a yau Talata za a gudanar da zaben shugabannin majalisu biyu na Wakilai da kuma Dattawa, tawagar gwamnonin ta isa zauren majalisar ta Tarayya da misalin karfe 9.45 na safiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel