Yanzu Yanzu: Ekweremadu ya dawo da motocin ofis

Yanzu Yanzu: Ekweremadu ya dawo da motocin ofis

Mataimakin Shugaban majalisar dattawa a majalisa ta takwas da suka kammala wa’adinsu kwanan nan, Ike Ekweremadu ya dawo da motocinsa na aiki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wakilinta da ya ziyarci wajen ajiye motoci na musamman na aka tanada saboda mataimakin Shugaban majalisar dattawar a safiyar ranar Talata, 11 ga watan Yuni ya hango motocin jere a wajen.

A ranar Litinin ne dai aka rahoto cewa Ekweremadu ya ki dawo da motocinsa na aiki duk da mulkinsu ya kare.

Sai dai wata majiya ta kusa da tsohon mataimakin Shugaban majalisar dattawar ta bayyana cewa an dawo da motocin ne a daren jiya Litinin bayan anyi masu sabis sannan aka wanke su.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Yadda zaben majalisar dokokin tarayya ke gudana

A wani labarin na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Uwargidar tsohon sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokoki na takwas, Sanata Shehu Sani ta gargadi mijin nara akan sadakar da alawus dinsa da zai samu ga yan gudun hijira da sauran mutanen da kashe-kashen arewacin kasar ya shafa.

Legit.ng ta rahoto cewa sanatan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 10 ga watan Yuni, a shafinsa na twitter, cewa martain matarsa tace kada yayi yunkurin sadakar da kowani bangare na alawus dinsa.

Yace a lokacin da ya gabatar masa da wani sako game da yadda Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya sadaukar da nasa alawus din ga iyalan Leah Sharibu da yan gudun hijira, sai tayi kamar bata karanta ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel