Ndume da Bago basu halarci ganawar da shugaba Buhari yayi da yan majalisan APC ba

Ndume da Bago basu halarci ganawar da shugaba Buhari yayi da yan majalisan APC ba

Rahotanni sun kawo cewa Sanata Mohammed Ali Ndume da Umar Bago basu halarci ganawar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi da yan majalisan APC ba a daren jiya Litinin, 10 ga watan Yuni.

An gudanar da taro daban-daban da zababbun yan majalisar dokokin tarayya wanda kwamitin masu ruwa da tsaki na APC suka kira aka kuma gudanar a waje guda.

Zababben sanata Ali Ndume, wanda ke kalubalantar Lawan, wajen tseren neman shugabancin majalisar dattawa, da dan majalisar wakilai Umar Bago, wanda ke kalubalantar Gbajabiamila wajen neman kujerar kakakin majalisar wakilai basu halarci ganawar ba.

Da yake Magana a wajen taron, Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole yace mafi akasarin wadanda ke kalubalantar hukuncin jam’iyyar a tsayar da yan takara sun amince su janye.

Oshiomhole yace har yanzu jam’iyyar na tattaunawa da sanata Ndume domin ya amince da hukuncinta don ra’ayin kasa da kuma mutunta Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Bikin rantsarwa: Okorocha ya isa majalisar dokoki, an ki tantance shi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa yayinda ake shirin gudanar da zaben majalisa, Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da zababbun yan majalisan dokokin tarayya na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a daren Litinin, 10 ga watan Yuni, 2019.

An kaddamar da wannan ganawa ne misalin karfe 9 na dare a dakin taron Ladi Kwali dake Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel