Hayakin injin janarato ya kashe mutane 6, ya bar mutane 23 cikin mawuyacin hali

Hayakin injin janarato ya kashe mutane 6, ya bar mutane 23 cikin mawuyacin hali

- Wasu 'yan biki su shida sun gamu da ajalinsu sanadiyyar shakar hayakin injin janarato da suka yi, yayin da kimanin mutane 30 suke kwance a asibiti cikin mawuyacin hali

- Mutanen an zo an tarar da su cikin wani mawuyacin hali da safe, indaa aka yi gaggawar garzayawa dasu asibiti domin ceto rayuwarsu

Rahotanni sun bayyana cewa mutane 6 ne suka rasa rayukansu, yayin da kimanin mutane 30 ke cikin mawuyacin hali bayan sun shaki hayakin injin janarato. Mutanen sun halarci wani bikin aure ne a Umuomumu, karamar hukumar Mbaitoli dake cikin jihar Imo.

A dauke wadanda lamarin ya shafa daga gidan bikin cikin mawuyacin hali.

KU KARANTA: Zaben 2019: Akwai matsala a nasarar da Buhari ya samu - Kungiyar kare hakkin dan adam

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Orlando Ikeokwu ya ce: "Da misalin karfe 8 na safe, wani mutumi mai suna Herbert Uzoegbu ya bayar da rahoton cewa dan uwanshi Raymond Uzoegbu, yayi taron bikin diyarshi a ranar 9 ga watan Yuni, wanda ya kai har daren ranar. Ya je gidan dan uwan nashi da safe domin ya duba shi, sai ya tarar da gidan a rufe, sai yayi ta kwankwasawa amma shiru babu wanda ya amsa.

"Sai ya haura gidan ya tarar da kowannensu cikin mawuyacin hali. Sai ya kira hukumar 'yan sanda, wadda DPO, Godwin Udom ya jagoranta, jami'an na zuwa suka garzaya da mutanen zuwa asibiti, a asibitin ne aka gano cewa mutane 6 sun mutu sannan kimanin 23 suna cikin tsaka mai wuya."

A cewarsa, kwamishinan 'yan sandan jihar, Rabiu Ladodo, ya bada umarnin gabatar da bincike akan lamarin domin gano ainahin abinda ya faru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel