Zaben 2019: Akwai matsala a nasarar da Buhari ya samu - Kungiyar kare hakkin dan adam

Zaben 2019: Akwai matsala a nasarar da Buhari ya samu - Kungiyar kare hakkin dan adam

- Kungiyar kare hakkin dan adam tace akwai matsala a samun nasarar da shugaba Buhari yayi a zaben da ya gabata

- Kungiyar tace an kashe sama da mutane 600 daga lokacin yakin neman zabe zuwa lokacin da aka kammala zabe

- Sai dai kuma har yanzu fadar shugaban kasa bata yi magana akan rahoton ba

Kungiyoyi a Najeriya sun soma mayar da martani akan sakamakon zaben shugaban kasa da kungiyar kare hakkin dan adam ta fitar a watannin baya, inda ta bayyana cewa nasarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu na cike da kalubale.

Rahoton ya bayyana cewa tun lokacin da aka fara yakin neman zabe a shekarar 2018 ake kara samun rikice-rikice a wasu jihohi na kasar nan, har ya zuwa lokacin da aka kammala zaben shugaban kasar a ranar 9 ga watan Fabrairu, 2019, kuma har yanzu gwamnati ta kasa daukar wani kwakkwaran mataki akan rikice-rikicen.

Kungiyar kare hakkin dan'adam din tace sama da mutane 600 ne suka rasa rayukan su sakamakon rikice-rikicen siyasa da kuma hare-hare da 'yan ta'addar Boko Haram suke kai wa wasu jihohi a yankin arewa maso gabas a lokacin zabe.

KU KARANTA: Mutanen Abuja sunyi Allah wadai da furucin shugaba Buhari a kansu

Hakazalika kuma rahoton yayi zargin cewa hatta 'yan sanda da sojoji da ya kamata ace sun kare mutane daga, suma suna da hannu a cikin kashe-kashen, ga kuma matsalar garkuwa da mutane da wasu ke yi domin samun kudin fansa, sannan ga harin 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma, duka wadannan sun taka muhimmiyar rawa wurin rikita lissafi a lokacin zaben, a yadda kungiyar ta bayyana ta ce lamarin ya fi kazanta a jihohin Kano da Rivers.

Sai dai kuma har ya zuwa yanzu fadar shugaban kasa bata ce komai game da rahoton ba, amma kuma mai magana da yawun gwamnatin jihar Kano, kamar yadda rahoton ya bayyana, Malam Aminu Yassar, ya bayyana cewa basu da masaniya akan yadda kungiyar ta samo wannan rahoton, saboda haka baza su ce komai akan sahihancinsa ba.

Amma kuma Yassar ya ce da gaske ne an samu rikice-rikice a tsakanin matasa lokacin zaben shugaban kasa dana gwamna da aka gabatar a jihar, sai dai kuma yayi zargi babbar jam'iyyar adawa ta PDP da kokarin tayar da zaune tsaye a lokacin zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel