Mafi yawan ‘yan takarar majalisa sun janyewa zabin Jam’iyya – Inji APC

Mafi yawan ‘yan takarar majalisa sun janyewa zabin Jam’iyya – Inji APC

A jiya Litinin, 10 ga Watan Yuni, 2019, ne manyan jam’iyyar APC su ka gana da ‘yan majalisa domin karkare duk wani shiri na zaben shugabannin majalisar tarayya da za ayi a Ranar Talata.

Kamar yadda labari ya zo mana, shugaban APC na kasa baki daya, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa da-dama daga cikin masu harin mukaman majalisar sun hakura saboda jam’iyya ta tsira.

Shugaban jam’iyyar yake cewa:

“Mu na alfahari da Sanatoci da-dama da ‘Yan majalisar tarayya da su ka hakura su ka janye takararsu, su ka amince da matakin da jam’iyya ta dauka, duk da cewa sun cancanci su rike wadannan kujeru.”

Oshiomhole ya na ganin cewa kowanen su ya isa ya rike mukami a majalisar.

“Duk sun hakura ne saboda jam’iyyar APC ta zauna lafiya.”

“Mu na godiya ga babban Sanata Danjuma Goje, wanda da kansa ya janyewa Ahmad Lawan. Na kuma zauna da Sanata Alimikhena wanda ya tabatar mani da cewa ya janyewa Omo Agege.

KU KARANTA: PDP ta dauki mataki a game da zaben Shugabannin Majalisa

“Hon. Yusuf Buba, Hon. Babangida Ibrahim, Hon. Odebunmi da Namdas duk sun janye takararsu. Shi ma Sanata Boroffice ya hakura da neman kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa.”

“A majalisar wakilai na tarayya, Onyejeocha Nkiru ta hakura da takarar da ta ke yi saboda Gbajabiamila. Haka zalika akwai masu neman kujerar mataimakin Kakaki da su ka janye takarar ganin jam’iyya ta zabi Wase.”

“Ina sa rai cewa Aboki na Sanata Ali Ndume ba zai tafi shi kadai ba, zai janye takarar da yake yi domin martabar jam’iyya da kuma ganin girman shugaban mu watau shugaban kasa Muhammadu Buhari.”

A karshen shugaban na APC ya ce:

“Ba na shakkar cewa Ali Ndume zai yi na’am, ya goyi bayan matakin da mafi yawan ‘yan jam’iyya su ka dauka.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel