Da dumi-dumi: Bikin rantsarwa: Okorocha ya isa majalisar dokoki, an ki tantance shi

Da dumi-dumi: Bikin rantsarwa: Okorocha ya isa majalisar dokoki, an ki tantance shi

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya isa harabar majalisar dokokin kasar da misalin karfe 7:40 na safe gabannin bikin rantsar day an majalisar.

An kaddamar da Okorocha a matsayin wanda ya lashe zaben sanata a yankin Imo ta yamma amma hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ki bashi takardar shaidar cin zabe.

Sai dai kuma wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a makon da ya gabata ta yi umurnin cewa a baiwa Okorocha takardar shaidar cin zabensa.

An tattaro cewa hukumar majalisar dokokin kasar bata tantance Okorocha ba domin ya samu dammar halartan bikin rantsarwar.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Yadda zaben majalisar dokokin tarayya ke gudana

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa har yanzu hukumar zabe na kasa watau INEC, ba ta ba Rochas Okorocha satifiket din lashe zabe ba.

Rochas Okorocha, yayi takarar Sanata a zaben 2019, har kuma yayi nasara, amma INEC ta ki mika masa takardar shaidar lashe zabe bayan jami’ar zaben ta ce cikin matsi ta sanar da nasarar APC.

Har yanzu dai hukumar ba ta cika umarnin kotu ba, yayin da ake shirin rantsar da majalisa ta tara a yau Talata, 11 ga Watan Yuni, 2019. INEC tace ta na duba lamarin ne har yanzu tukuna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel