APC ta tsayar da mutumin daya saci sandan majalisa a matsayin mataimakin shugaban majalisa

APC ta tsayar da mutumin daya saci sandan majalisa a matsayin mataimakin shugaban majalisa

Shugabancin jam’iyyar APC ta sanar da amincewa da Sanata Ovie Omo-Agege a matsayin dan takarar mataimakin shugaban majalisar dattawa ta tara, kamar yadda kaakakin jam’iyyar, Lanre Issa-Onilu ya bayyana.

Legit.ng ta ruwaito Onilu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, 10 ga watan Yuni a sakatariyar jam’iyyar APC dake babban birnin tarayya Abuja, inda yace jam’iyyar ta yanke wannan shawara ne bayan zaman gaggawa da tayi.

KU KARANTA: Masu uwa a gindin murhu: Yaron tsohon gwamna, kuma Sanata a yanzu ya zama kaakakin majalisa

Haka zalika kaakakin yace jam’iyyar ta amince da takarar dan majalisa mai wakiltar mazabar Wase ta jahar Jos, Idris Maje a matsayin mataimakin kaakakin majalisar wakilai. Mista Onilu yace jam’iyyar ta yanke shawarar ne bayan tattaunawa da shugaban kasa Buhari, gwamnoni da masu ruwa da tsaki.

“Muna kira ga kafatanin yayan jam’iyyar APC dake majalisar wakilai da majalisar dattawa dasu kasance masu biyayya ga umarnin uwar jam’iyya, muna kira ga wadanda suka bayyana burin neman wasu mukamai dasu goyi bayan wadanda jam’iyya ta tsayar.” Inji shi.

Sanata Ovie Omo-Agege yana wakiltar mazabar Delta ta tsakiya ne, kuma haifaffen kauyen Orogun ne dake cikin karamar hukumar Ughelli ta Arewa, wanda ake sa ran zai zama sabon mataimakin kaakakin majalisar a ranar Talata, 11 ga watan Yuni.

A wani labarin kuma, gwamnonin jam’iyyar APC sun bayyana goyon bayansu ga mutanen da jam’iyyar APC ta tsayar a matsayin shuwagabannin majalisun dokokin Najeriya, Sanata Ahmad Lawan da Omo-Agege a majalisar dattawa da Femi Gbajabiamila da Idris Maje a majalisar wakilai.

A ranar Talata, 11 ga watan Yuni ne sabuwar majalisa ta tara zata fara zamanta kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci akawun majalisar, haka nan yan majalisun zasu zabi shuwagabannin majalisar a yau.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel