Ina taya Ogundoyin murnar zama Kakakin Majalisa – Inji Davido

Ina taya Ogundoyin murnar zama Kakakin Majalisa – Inji Davido

Fitaccen Mawakin nan na Najeriya, Mista David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya fito yayi magana bayan Debo Ogundoyin ya zama sabon kakakin majalisar dokoki na jihar Oyo.

David Adeleke ya taya sabon shugaban majalisar jihar ta Oyo murnar lashe zaben kakakin da yayi jiya, 10 ga Watan Yuni, 2019. Davido ya bayyana wannan ne a shafin sa na sadarwa na Tuwita.

Shararren Mawakin yake cewa sun yi aiki tare da Debo Ogundoyin a baya. Davido ya bayyana cewa sabon kakakin majalisar ya kasance Manajansa a lokacin da su ke kamfanin DremoDrizzy.

Adeleke yayi duk wannan bayani ne a shafinsa na Tuwita bayan labari ya bazu cewa Matashin ne zai rike majalisar dokokin jihar Oyo. ‘Yan majalisar kaf ne su ka yi masa mubaya’a a zaben na jiya.

KU KARANTA: 'Yan Majalisan PDP za su zabi Ahmad Lawan - Sanatan APC

Davido yayi amfani da Tuwita ya rubuta:

“Ina sha'awar ganin Mutum ya cin ma burinsa a rayuwa. Shekaru 3 da su ka wuce, mu na aiki tare da kai a kamfanin DremoDrizzy…”

Mawakin ya cigaba: “…Yau ga shi ka zama kakakin majalisar dokoki na jihar Oyo. Ina taya ka murna, kuma ina alfahari da kai…”

Rt. Hon. Debo Ogundoyin mai shekaru kusan 30 a Duniya shi ne mai wakiltar Ibarapa ta Gabas a majalisar dokokin jihar, yayi nasarar zama shugaban majalisar ne a karkashin jam’iyyar PDP.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel