Majalisa ta tara: Onyejeocha ta janye daga takarar kakakin majalisa

Majalisa ta tara: Onyejeocha ta janye daga takarar kakakin majalisa

Mace tilo dake takara kakakin majalissar tarayya a sabuwar majalisa, Nkeiruka Onyejeocha, ta janye daga takarar.

Ta bayyana hakan ne a jawabin da aka fitar ga yan jarida a daren ranar litinin 10, yuni 2019, kasa da awa 24 da za a kaddamar da majalisar ta tara.

Onyejeocha ta bayyana cewa dalilanta na da nasaba ne da tabbaci da ta samu daga jamiyyar APC cewa za a tafi da ita da kuma bangaren da take wakilta a sabuwar majalisar.

A bisa haka ne ta bayyana goyan bayanta ga Femi Gbajabiamila, dan takarar shalele na APC.

Bayanin na cewa kamar haka " Na bayyana niyyata ta takara domin inganta tsarin aiki majalisa wanda zai kawo cigaban kowa da kuma adalci a najeriya, musamman ga wa'yanda ake ma wariya kamar talakawan mata da matsa, wa'yanda ke kukan a rika sanya su wajen tafiyar da tattalin arzikin najeriya da sauran sha'anin kasa."

Karanta wannan: An zabi dalibin makaranta dan shekara 33 mukamin kaakakin majalisar Filato

"Sanin kowa ne kuma, na shiga wannan takara ne saboda yanki na na kudu maso gabacin najeriya, don magance ikikarin da akeyi cewa jam'iyyar mu na nuna wariyar yanki, don kuma tabbatar da an samu daidaito wajen mulkin najeria daga dukkan yankun kasarmu."

Yar majalissar ta bayyana cewa tana sane da matsayar jam'iyyar su tun farko, amma ta shiga takarar ne sabida ware yankinta na kudu maso gabacin najeria da kuma jinsin mata da akayi.

"Sabida haka zan janye takarata da fatan cewa tabbacin da shuwagabannin jam'iyyarmu da abokanan aiki na suka bani na cewa za a rinka sauraren ra'ayoyin yankina na kudu maso gabacin najeria da matan najeriya baki daya, wajen gudanar da sha'anin majalisar."

Ta kara da cewa "ina da yakinin cewa wannan tabbaci da aka bani da kuma kamfen din da nayi ya kara wayar da kan jam'iyyata sanin mahimmacin tafiya da yankin kudu maso gabacin najeria da kuma mata wajen gudanar da mulkin kasa a wannan shekaru hudun masu zuwa."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel