2019: INEC ta hana Okorocha satifiket duk da umarnin babban Kotu

2019: INEC ta hana Okorocha satifiket duk da umarnin babban Kotu

A dadai lokacin da ake shirin rantsar da sabuwar majalisar tarayya, mun samu labari cewa har yanzu hukumar zabe na kasa watau INEC, ba ta ba Rochas Okorocha satifiket din lashe zabe ba.

Rochas Okorocha, yayi takarar Sanata a zaben 2019, har kuma yayi nasara, amma INEC ta ki mika masa takardar shaidar lashe zabe bayan jami’ar zaben ta ce cikin matsi ta sanar da nasarar APC.

A karshe dai wani babban kotun tarayya da ke zama a Garin Abuja ya nemi INEC ta ba tsohon gwamnan na jihar Imo satifiket din da ke tabbatar da shi a matsayin zababben Sanatan kasar.

Har yanzu dai hukumar ba ta cika wannan umarni ba, yayin da ake shirin rantsar da majalisa ta tara a yau Talata, 11 ga Watan Yuni, 2019. INEC tace ta na duba lamarin ne har yanzu tukuna.

KU KARANTA: Zaben Majalisa: Jam’iyyar PDP ta fitar da matsaya a Ranar karshe

Rashin wannan satifiket zai hana Rochas Okorocha shiga majalisar dattawan, har yayi kokarin kada kuri’ar sa a zaben da za ayi. Okorocha yana ganin dai wasu ne a APC ke shirya masa tuggu.

A jawabin da tsohon gwamnan na APC ya fitar ta bakin wani Hadminsa, Sam Onwumedo, ya karyata cewa INEC ta ba sa satifiket din sa a hannu. Okorocha yace babu gaskiya a wannan labari.

Okorocha ya kara da cewa da zarar takardar lashe zaben na sa ya shigo hannunsa, zai sanar da Duniya. Yanzu dai za a kafa gwamnati, yankin Imo ta Yamma ba su da wakili a majalisar dattawa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel