Masu uwa a gindin murhu: Yaron tsohon gwamna, kuma Sanata a yanzu ya zama kaakakin majalisa

Masu uwa a gindin murhu: Yaron tsohon gwamna, kuma Sanata a yanzu ya zama kaakakin majalisa

Da ga tsohon gwamnan jahar Abia Theodore Orji, Chinedum Orji ya lashe zabe a majalisar dokokin jahar Abia wanda hakan ya bashi daman darewa mukamin kaakakin majalisar dokokin jahar, inji rahoton jarida The Cable.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Orji wanda shine tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar ya zama kaakakin majalisa ne bayan dan majalisa dake wakiltar mazabar Ugwunagbo, Munachin Alozie ya gabatar da kudurin hakan gaban majalisar.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai hari jami’ar Filato, sun bindige dalibi har lahira

Masu uwa a gindin murhu: Yaron tsohon gwamna, kuma Sanata a yanzu ya zama kaakakin majalisa

Chinedum
Source: Twitter

Ba tare da wata wata ba shima wani dan majalisa dake wakiltar mazabar Isialangwa, Ginger Onwusibe ya mara ma kudurin Munachin baya, daga nan suma sauran takwarorinsu yan majalisa suka mika wuya.

Mahaifin sabon kaakakin majalisar, Theodore ya taba zama gwamnan jahar Abia daga shekarar 2007 zuwa 2015, haka zalika a yanzu haka shine sabon zababben Sanatan mazabar Abia ta tsakiya a majalisar dattawa.

A jawabinsa, Orji yace majalisar ba zata zamto yar amshin shata ba; “Jama’a suke zabemu, don haka mu na jama’a ne, kuma zamu tabbata mun saka bukatun jama’a a gabanmu, don haka a shirye muke wajen samar da sahihan dokoki da zasu taimaki jama’a.

“Bugu da kari zamu baiwa gwamnatin Gwamna Victor Ikpeazu goyon baya dari bisa dari domin cimma manufarsa ta inganta jahar Abia, zamu sanya kafar wando daya da duk wani jami’in gwamnati da muka samu da laifin cin dunduniyar gwamnan.” Inji shi.

Sauran jagororin majalisar da aka zaba sun hada da Ifeanyi Uchendu wanda ya zamo mataimakin kaakakin majalisa, Solomon Akpulonu daya zama shugaban masu rinjaye da Munachim Alozie sabon bulaliyar majalisa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel