Buhari zai yi sabbin nade-nade bayan bikin ranar Dimokuradiyya

Buhari zai yi sabbin nade-nade bayan bikin ranar Dimokuradiyya

-Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa an riga da an kammala dukkanin shirye-shirye domin gudanar da bikin Ranar Dimokuradiyya a kasar.

-A cewar hadimin shugaban kasar, daga yau ranar 29 ga watan Mayu ta tashi daga ranar hutu yayin da aka maida 12 ga watan Yunin ko wace shekara ranar hutu ta Dimokuradiyya.

Shugaba Muhammadu Buhari zai sanar da nadin sabbin mukamai bayan an kammala bikin Ranar Dimokuradiyya ta kasa kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro mana.

A jiya Litinin ne Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan dokar mayar da 12 ga watan Yunin ko wace shekara matsayin ranar hutu a kasar nan.

KU KARANTA:'Yan majalisa 6 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Imo

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan lamuran majalisa, sanata Ita Enang ne ya shaidawa manema labarai wannan batu yayin da yake ganawa dasu a fadar shugaban kasa.

Ya ce: “ Sanya hannun da shugaban kasa ya yi kan wannan dokar ya kore ranar 29 ga watan Mayu matsayin hutu zuwa ga 12 ga watan Yuni daga yau.”

“ Daga yau, 29 ga watan Mayu ta tashi daga ranar hutu, yanzu ranar Dimokuradiyya a kasar nan ita ce 12 ga watan Yuni”, a cewarsa.

Bugu da kari, 29 ga watan Mayu na nan a matsayin ranar rantsar da sabuwar gwamnati. Wannan sanya hannu ya zo ne akalla kimanin saura awa 24 kafin bikin ranar dimokuradiyya a Najeriya wanda zai gudana a Eagle Square, Abuja.

Wata majiya da ta fito daga fadar shugaban kasa ta ce: “An riga an kammala dukkanin shirye-shirye na wannan biki. Akwai shugabannin duniya da aka gayyata kuma ana tsimayen halartarsu.”

Majiyar ta cigaba da cewa: “ A wurin wannan bikin ne Shugaba Buhari zai bayyana shirinsa da kuma abinda wa’adinsa na biyu zai karkata a kai. Haka zalika ana sa ran daga an kammala wannan biki shugaban kasa zai sanar da sabbin nade-naden mukamai na gwamnatinsa.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel