2019: Babu wani sabani tsakanin mu da Ndume – Jirgin yakin Lawan

2019: Babu wani sabani tsakanin mu da Ndume – Jirgin yakin Lawan

Yayin da bai wuce wasu sa’o'i kadan a rantsar da shugabannnin majalisar tarayya a Najeriya ba, kwamitin yakin neman zaben Sanata Ahmad Lawan, ya fito ya sake bada tabbacin lashe zaben da za ayi.

Shugaban kamfen din Ahmad Lawan, Sanata Yahaya Abdullahi ya bayyana cewa shakka babu, Lawan ya ci zabe ya gama. Sanatan ya bayyana wannan ne a wata hira da yayi a birnin tarayya Abuja.

Yahaya Abdullahi yace Ahmad Lawan ne zai zama shugaban majalisar dattawa da nufin Ubangiji. Abdullahi yana mai cewa akwai yakinin cewa za su yi nasara a zaben da za ayi Ranar Talata 11 na Yuni.

Sanatan ya fadawa Manema labarai cewa sun hango nasarar Sanata Ahmad Lawan ne tun kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar su ta APC mai mulki su sa baki cikin tafiyar.

Shugaban jirgin yakin na neman zaben Ahmad Lawan yayi wannan jawabi ne a Ranar Litinin, 10 ga Watan Yuni, 2019, yana cewa:

KU KARANTA: Zaben Majalisa: Jam’iyyar PDP ta fitar da matsaya a yau

“Mun yi bakin kokarin mu na ganin Ahmad Lawan yayi nasara. Tun kafin mu ci albarkacin Buhari da jam’iyyar mu ta APC, mu ka fara yakin neman zabe.”

“Duk da mara mana bayan da Uwar jam’iyya tayi, mun tashi tsaye wajen samun goyon bayan sauran abokan aikin mu daga jam’iyyar hamayya da ma APC.”

“PDP ta na da Sanatoci har 44 a cikin 109 da ke majalisa don haka dole mu ka zauna da su. Mun gana da su daya-bayan-daya, kuma mun yi zama a gungu…”

“…Mun hadu da ‘yan majalisar PDP a gidan Sanata Ike Ekweremadu inda aka yi raha da ba’a. Sanatocin PDP sun san cewa Lawan ya cancanci ya rike wannan mukami…”

“Yan majalisar na PDP za su yi adalci su marawa Ahmad Lawan baya.”

A game da Ndume kuwa:

“Babu wani rikici tsakanin mu da shi, Abokan aiki ne mu, ba wai Abokan fada ba."

“Ya na da damar yin takara… mu na masa fatan alheri.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel