Yan bindiga sun kai hari jami’ar Filato, sun bindige dalibi har lahira

Yan bindiga sun kai hari jami’ar Filato, sun bindige dalibi har lahira

Wasu gungun mahara yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun kai farmaki cikin jami’ar jahar Filato dake garin Bokkos, inda suka bindige wani dalibi har lahira, sa’annan suka raunata wani dalibin a sanadiyyar harbin bindiga.

Rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito yan bindigan sun kai wannan hari ne a daren Lahadi, 9 ga watan Yuni, inda shigarsu jami’ar keda wuya suka zarce kai tsaye zuwa dakunan kwanan dalibai inda suka aikata aika aika.

KU KARANTA: Matashin dan siyasa ya dare mukamin kaakakin majalisar dokokin jahar Oyo

Rahotanni sun bayyana sunan dalibin da aka kashe a matsayin Sheni Kimati, dan shekara 25, dalibin aji 2 daga sashin ilimin Geography, inda ya rasu bayan an garzaya dashi zuwa Asibiti a sanadiyyar raunin harbin bindiga daya samu daga yan bindigan.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban jami’ar, Farfesa Yohanna Izam ya yi kira ga dalibansu dake cikin matsanancin halin firgici dasu kwantar da hankulansu domin kuwa jami’an tsaro sun bazama farautan yan bindigan.

“Dukanmu mun kadu da wannan hari, lamarin yayi matukar bamu mamaki, hukumar jami’ar na mika ta’aziyyarta ga iyalan wadanda harin ya shafa, don haka akwai bukatar mu baiwa Sojoji hadin kai don su gano miyagun mutanen nan, bamu son sake aukuwar wannan lamari.” Inji Farfesa Izam.

Shima kaakakin rundunar Yansandan jahar, Terna Tyopev ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace da misalin karfe 11 na daren Lahadi ne yan bindigan suka yi ma jami’ar tsinke, sai dai yace har yanzu basu kama kowa ba tukunna.

Don haka ya nemi duk wani wanda keda masaniya game da yan bindigan daya taimaka ma Yansanda da bayanai da zasu kai ga kamo miyagun yan bindigan domin su fuskanci hukuncin laifin da suka aikata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel