Kotu ta umurci ayi yar tinke a zaben Majalisar tarayya

Kotu ta umurci ayi yar tinke a zaben Majalisar tarayya

Babbar kotun Abuja ta mai shari'a O.A Musa ta dakatar da magatakardan majalissar dattawa, da kuma da kuma babban jami'in tsaro da gunarwa na majalisa daga yin amfani da dokokin majalisa na shekarar 2015 wajen gudanar da zaben majalisa ta tara.

Kotun ta umarci majalissar dattawa da tayi amfani da dokokin majalisar na 2011 wanda ya bada tsarin yin zaben shuwagabannin majalisar ta hanyar budaddiyar kuri'a.

An bayar da umarnin ne bayan da kotun ta saurari kudiri mai namba M/266/2019 wanda Ebere Nwanya Esq, lauyan sanata Jibrin Bara'u ya shigar.

Karanta wannan: 2019: Babu wani sabani tsakanin mu da Ndume – Jirgin yakin Lawan

Idan za a iya tunawa, sanatocin APC sun aibanta yin amfani da dokokin majalisa na 2015 inda suke ikirari cewa tsofaffin shuwagabannin majalisar dattawa sun cusa yin amfani da kuri'ar sirri wajen gudanar da zabe ba tare da yardar sauran mambobin majalisar ba.

kotun ta dage sauraren zuwa ranar Alhamis, 13 Yuni, 2019 don sauraren cikakkiyar shari'ar.

Wannan umarni na zuwa ne yayin da ake gab da gudanar da zaben majalisar wanda za a gudanar yau Talata, 11 ga watan Yuni 2019.

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel