An zabi dalibin makaranta dan shekara 33 mukamin kaakakin majalisar Filato

An zabi dalibin makaranta dan shekara 33 mukamin kaakakin majalisar Filato

Wani matashi mai shekaru 33, Abok Ayuba ya kasance sabon zababben kaakakin majalisar dokokin jahar Filato bayan samun goyon baya da kuma amincewar sauran takwarorinsa yan majalisa.

Legit.ng ta ruwaito sabon kaakaki Abok Ayuba dalibin ajin karshe ne a tsangayar ilimin sharia ta jami’ar Jos dake garin Filato, kuma shine wakilin al’ummar mazabar Jos ta gabas a karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki.

KU KARANTA: Matashin dan siyasa ya dare mukamin kaakakin majalisar dokokin jahar Oyo

An zabi dalibin makaranta dan shekara 33 mukamin kaakakin majalisar Filato

Abok Ayuba
Source: Facebook

Abokin aikinsa dake wakiltar mazabar Jos ta Arewacin Arewa a majalisar, Ibrahim Baba-Hassan ne ya fara bayyana dacewar zaben Abok Ayuba a matsayin sabon kaakakin majalisar dokokin jahar Filato ta tara, yayin da Simi Dusu daga mazabar Arewa maso kudancin Jos ya mara masa baya.

Mista Abok Ayuba da ire irensa masu karancin shekaru da ake ganin matasa ne sun samu tagomashi a siyasar Najeriya ne albarkacin dokar rage shekarun tsayawa takara ta ‘Not too young to run’ da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattafa ma hannu.

Da wannan doka aka rage shekarun daya kamata mutum ya kai kafin ya tsaya takarar dan majalisar dokokin jaha daga shekara 30 zuwa shekara 25, da haka aka samu yan majalisar dokoki 22 a fadin Najeriya da basu haura shekara 30 ba.

Dayake jawabi bayan darewa mukamin Kaakakin majalisa, Ayuba ya bayyana godiyarsa ga takwarorinsa bisa amincewa da suka yi dashi na shugabantarsu, sa’annan yayi alkawarin ba zai basu kunya sakamakon jagoranci nagari daya kudurci nunawa a majalisar.

A wani labarin kuma, wani matashin dan siyasa dan shekara 32 mai suna Adebo Ogundoyin dake wakiltar mazabar Ibarapa ta gabas ta jahar Ibadan ya zama sabon kaakakin majalisar dokokin jahar ta tara, ba tare da wata hamayya ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel