Manyan Arewa ke kara girman talauci a yankin - Moghalu

Manyan Arewa ke kara girman talauci a yankin - Moghalu

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar YPP a zaben 2019 na bana, Farfesa Kingley Moghalu, ya zargi manyan Arewa da kuma 'yan siyasar yankin da kara girman talauci a kan al'ummar su a sanadiyar soyuwar zukatan su.

A cewar Farfesa Moghalu, son zuciya da ya mamaye manyan Arewa da kuma 'yan siyasar su, shi ne musabbabin da ke kara girman talauci gami da haifar da rashin ci gaba a yankin.

Cikin jawaban da ya gabatar, Farfesa Moghalu ya bayyana hakan ne yayin halartar wata lacca a kan ci gaban al'umma ta shekara da aka gudanar a babban dakin taro na asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano dake birnin Kanon Dabo.

Farfesa Moghalu ya bayyana mamakin sa gami da damuwa dangane da yadda katutu na talauci ya zamto tamkar wata alama a kan al'ummar Arewa duba da yadda suka ci gaba da samar da jagorori a kasar nan tsawon shekaru 42 kawo wa yanzu.

Da ya ke ci gaba da bayyana takaicin sa a kan yadda Arewacin Najeriya ya zamto wata babbar hedikwata ta talauci a Najeriya, ya shawarci manyan 'yan siyasa da masu riko da madafan iko a kan yiwa kawunan su karatun ta nutsu wajen tabbatar da ci gaba a yankin.

KARANTA KUMA: Harin Boko Haram ya salwantar da rayukan dakarun Kamaru a gabar tafkin Chadi

Ya kuma bayar da shawara ta yakar ta'ammali da miyagun kwayoyi tare da samar da ayyukan yi musamman a tsakankanin matasa, inganta jin dadin rayuwar Mata, bunkasa harkokin ilimi gami da dawo da martabar masana'antu musamman a jihar Kano da ta kasance cibiyar kasuwanci.

Cikin wani rahoto mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, mujallar tattalin arziki wadda ake bugawa a kasar Birtaniya, Economist, ta ce 'yan Najeriya sun kara yin nutso cikin kangi na talauci a mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel