2019: Cikin tsanani na rikicin zabe Buhari ya samu nasara - HRW

2019: Cikin tsanani na rikicin zabe Buhari ya samu nasara - HRW

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe babban zaben kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu cikin mafi kololuwar tsanani na tashin tashina da rikicin zabe kamar yadda kungiyar kare hakki dan Adam HRW ta bayyana.

Cikin rahoton da kungiyar HRW (Human Rights Watch) ta fitar da wallafar sa a ranar Litinin, ta zargi hukumomin tsaro na 'yan sanda da kuma dakarun soji a kan bayar da gudunmuwar tayar da tarzoma a kasar nan yayin babban zabe.

Kungiyar mai kare hakkin dan Adam ta duniya ta ce miyagun ababen sun mamaye babban zaben kasar nan da suka hadar da ta'azzarar aukuwar hare haren Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas, rikicin makiyaya da manoma a Kudu da kuma Arewa ta Tsakiya da kuma ta'adar masu garkuwa da mutane a jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna.

Kungiyar ta kuma buga misalai da yadda hukumomin tsaro suka gaza sauke nauyn da ya rataya a wuyan su musamman gabanin zabe a jihar Ribas da Kano, inda aka ci zarafin 'yan jarida, masu jefa kuri'u da kuma ma'aikatan zabe.

Wakiliyar kungiyar HRW reshen Najeriya, Ms Anietie Ewang, ta bayar da shaidar wannan rahoto inda ta ce babu wani ci gaba na ingancin tsaro da aka samu yayin zaben bana na 2019 idan an kwatanta da zabukan da suka shude a tarihi.

KARANTA KUMA: Manyan Arewa ke kara girman talauci a yankin - Moghalu

Ta nemi shugaban kasa Buhari da ya daura damara tare da sanya sulken kawo sababbin tsare-tsare a wa'adin sa na biyu wajen magance aukuwar wannan mummunan lamari yayin gudanar da zabukan kasar nan a gaba domin tabbatar da martabar kasar Najeriya a idon duniya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel