Dino Melaye ba zai iya galaba a kaina ba – Yahaya Bello

Dino Melaye ba zai iya galaba a kaina ba – Yahaya Bello

-Yayinda zaben gwamnan Jihar Kogi ke sake kusantowa, Yahaya Bello ya nuna cewa babu aninda Dino Melaye zai iya yi domin karbe kujerar gwamna daga hannunsa.

-Ba wai muna tunanin nasara a zabe mai zuwa bane, a'a muna lissafin tazarar da zamu bai wa jam'iyar da zata kasance a mataki na biyu ne lokacin zaben, a cewar gwamna Bello.

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya yi magana a kan takarar da sanata ma wakiltar Kogi ta tsakiya ya tsaya, a matsayin mai son zama gwamnan jihar a zabe dake tafe ranar 16 ga watan Nuwamban 2019.

Gwamnan ya bayyana cewa, “ Tabbas abinda sanatan ke shirin yi ba abu bane mai sauki a gare shi ba.” Ya yi wannan furucin ne ga ‘yan jarida a Abuja bayan gwamnonin jam’iyar APC sun kammala wata ganawa ta musamman a daren ranar Lahadi.

KU KARANTA:Harin Boko Haram ya salwantar da rayukan dakarun Kamaru a gabar tafkin Chadi

Da yake amsa tambaya game da ko sanata Dino zai iya galaba a kansa, Bello ya ce: “ A duk lokacin da za kuyi magana kuyi maganar mutanen kirki. A kan kuma wannan wanda kuke magana kansa, ya fara cika alkawarin da yayi wa yankinsa kafin yazo ya ce zai yi takara dani, domin yin hakan tamkar daukar dala ba gammo ne a gareshi .”

Har wa yau, gwamna ya bada tabbacin cewa: “ Ina da yaqinin cewa ni zan kasance dan takarar APC a zaben gwamna mai zuwa na jaharmu, idan bani aka ba tikiti ba to wa za’a bai wa?”

“ Zabe na gabatowa a Kogi, mutane da dama zasu kalubalance mu. Amma abu mafi gaskiya shi ne a shirye muke, ba wai kawai muna maganar lashe zaben ne kadai ba, muna maganar irin tazarar da zamu ba duk jam’iyar dake bin mu a baya a zaben mai zuwa. Hakan kuma zai kasance ne a dalilin cika alkawuranmu da mu kayi a jihar.” Kamar yadda Bello ya ce.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel