'Yan bindiga sun kashe mutane 12 a harin da suka kai Shiroro

'Yan bindiga sun kashe mutane 12 a harin da suka kai Shiroro

A kalla mutane 12 ne suka mutu bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari a kan jama'ar garuruwan yankin Kwaki a mazabar Chukuba da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewar 'yan bindigar sun kai harin ne a kan mutanen kauyukan Ajatayi, Gwassa da Barden Dawaki a ranar Lahadi. Harin na zuwa ne kwanaki hudu bayan 'yan bindigar sun kai wani farmaki a kauyukan Gyammamiya da Alewa.

Jaridar Daily Trus ta rawaito cewar 'yan bindigar sun sace a kalla shanu 525 bayan jama'ar kauyukan sun gudu domin tsira da rayuwarsu.

Sanata mai wakilatr yankin da 'yan bindigar suka kai harin, David Umaru, ya bayyana cewar ya samu kiraye-kiraye daga jama'a da dama tun bayan kai harin kwanaki uku da suka wuce.

Ya kara da cewa tuni ya sanar da jami'an tsaro abinda ya faru domin daukan matakin da ya dace.

DUBA WANNAN: Bata ruwa: Gwamnan PDP da Sanatocin jam'iyyar sun shiga ganawa a gaggau ce

Da yake tabbatar da labarin kai harin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Neja, DSP Abubakar Dan-Ina, ya ce mutum daya ne 'yan bindigar suka kashe tare da raunata wasu 15 yayin harin.

Ya ce 'yan bindigar sun sace shanu tare da far wa duk wanda ya zo kusa da su saboda tsoron kar a kama su.

Ya bayyana cewar lamarin ya faru ne a kauyukan Ajapayi da Kwaki a karaar hukumar Shiroro tare da bayar da tabbacin cewar rundunar 'yan sanda ta shawo kan lamarin duk da wuyar zuwa da kauyukan ke da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel