Bata ruwa: Gwamnan PDP da Sanatocin jam'iyyar sun shiga ganawa a gaggau ce

Bata ruwa: Gwamnan PDP da Sanatocin jam'iyyar sun shiga ganawa a gaggau ce

A yayin da ake shirin rantsar da majalisar tarayya a ranar Talata, 11 ga watan Yuni, jam'iyyar PDP ta kir wani taron gaggawa da dukkan mambobin majalisar dattijai da aka zaba a karkashin tutar jam'iyyar.

Taron da jam'iyyar ta kira ranar Litinin da misalin karfe 8:00 na daren ranar Litinin na cigaba da gudana har a lokacin da aka wallafa wannan rahoto. Ana yin taron ne a gidan gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, dake unguwar Asokoro a Abuja.

Sakon gayyatar zababbun Sanatocin na dauke da sako kamar haka: "ya mai girma zababben sanata a jam'iyyar PDP, mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Ike Ekweremadu, ya umarce ni na gayyace ku zuwa muhimmin taro tare da gwamna Wike a yau."

Jaridar Tribune ta ce majiyar ta da ke da kusanci da wasu daga cikin sanatocin ta shaida mata cewar an kira taron ne domin wargatsa shirin jam'iyyar APC na ware 'yan takarar da take so a zaba a kujerun shugabancin majalisar dattijai.

Da yake bayyana salon yakin neman zaben jam'iyyar APC a matsayin na makirci, Sanata Emmanuel Bwacha ya ce: "akwai dattako a yin shiru, sannan akwai makirci a wurin mai yawan surutu. Mun yi shiru ne saboda bama son a samu hayaniya a majalisa ta 9."

Da yake amsa tambaya a kan rahoton cewar wasu sanatocin jam'iyyar PDP sun goyi bayan dan takarar da APC ta tsayar, Bwacha ya ce: "ba ma magana a tsinke, 'yan uwa ne mu da ke magana da murya daya saboda kan mu a hade ya ke."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel