Shugaba Buhari ya samu nasara ta farko a kotun sauraron korafin zabe

Shugaba Buhari ya samu nasara ta farko a kotun sauraron korafin zabe

Jam'iyyar 'Coalition 4 Change' (C4C) da dan takarar ta na shugaban kasa a zaben da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabrairun 2019 sun janye karar da suka shigar na kalubalantar sakamakon zaben ya bayyana shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya sake samun nasara.

C4C da dan takarar ta sun janye karar ne daga kotun sauraron korafe-korafe a kan zaben shugaba kasa a ranar Litinin.

Kotun ta kori karar da jam'iyyar C4C da dan takarar ta, Geff Ojinika, suka shigar bayan sun mika takardar neman hakan.

A takardar su da suka shigar da kara, mai adireshi CA/PEPC/003/2019, sun roki kotun da ta soke zaben shugaban da ya samar da shugaba Buhari a matsayin wanda ya yi nasara bisa zargin cewar zaben cike yake da saba dokokin zabe da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2010.

Jastis Mohammed Garba, sabon alkalin dake sauraron korafe-korafe a kan zaben shugaban kasa, ya amince da bukatar C4C da dan takarar ta na korar karar da suka shigar kammar yadda suka nema ta bakin lauyansu, Mista Obed Agu.

DUBA WANNAN: Bata ruwa: Gwamnan PDP da Sanatocin jam'iyyar sun shiga ganawa a gaggau ce

Jastis Garba, sabon alkalin da ya maye gurbin Jastis Zainab Bulkachuwa, ya ce karar ta tabbata korarriya tunda babu wani mai korafi a kan hakan.

Da yake magana da manema labarai bayan zaman kotun, Agu ya ce wadanda yake wakilta sun janye karar ne bayan ganawar kwamitin zartar wa (NEC) na jam'iyyarsu ya yanke shawar bayar da gudunmawarsa wajen cigaban dimokradiyya a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel