Zaben 2019: Janye karar kalubalantar nasarar Buhari ta farantawa fadar shugaban kasa

Zaben 2019: Janye karar kalubalantar nasarar Buhari ta farantawa fadar shugaban kasa

Daya daga cikin korafe korafe hudu masu kalubalantar sakamakon babban zaben shugaban kasa ya watse yayin da jam'iyyar C4C (Coalition for Change) ta janye karar rashin amincewa da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Fadar shugaban kasa a ranar Litinin ta bayyana farin cikin ta yayin da jam'iyyar C4C ta janye karar kalubalantar nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta babban zaben kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

A yayin haka fadar shugaban kasa ta yabawa jam'iyyar C4C dangane da janye korafin ta na kalubalantar nasarar shugaban kasa Buhari yayin zaman kotun daukaka karar zabe da aka dawo da ci gaban sa a ranar Litinin bisa jagorancin Justice M.L Garba.

Mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu, shi ne ya bayar shaidar hakan a garin Abuja. Ya yabawa kwazon jam'iyyar C4C da ya misalta a matsayin mafi kololuwar kishin kasa tare da cewar ta fahimci gaskiya gami da daukar dangana ta kaddara.

KARANTA KUMA: Kakakin Majalisa: Onyejeocha da Odebunmi sun janye wa Gbajabiamila takara

Yayin neman goyon bayan dukkanin masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da ci gaban kasa, babban hadimin shugaban kasar ya kara da cewa zaben 2019 ya tabbatar da yadda al'ummar Najeriya suka sanya aminci a kan jagorancin shugaban kasa Buhari.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Justice M.L Garba ya maye gurbin Justice Zainab Bulkachuwa a a matsayin shugaban kotun daukaka karar zaben shugaban kasa biyo bayan zame hannun ta da tayi tun a ranar 22 ga watan Mayu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel