Da duminsa: Jirgin Sojin sama ya ragargaza sansanin yan Boko Haram a Sambisa

Da duminsa: Jirgin Sojin sama ya ragargaza sansanin yan Boko Haram a Sambisa

Dakarun sojin saman Operation LAFIYA DOLE sun kai mumunan hari kan yan tada kayar bayan Boko Haram a unguwar Alafa dake cikin dajin Sambisa, jihar Borno a ranar Litinin, 10 ga watan Yuni, 2019.

Kakakin hukumar sojin saman, Bimbo Daramola, ya bayyana wannan ne a wani jawabin da ya saki da yammacin yau Litinin, yace:

"Dakarun sojin sama na rundunar Operation lafiya dole sun samu wani nasara kan yan ta'addan Boko Haram dake zaune a dajin Sambisan jihar Borno."

"Harin wanda ya kai ga ragargaza babbar cibiyar taronsu tare da hallaka yan ta'adda da dama, ya gudana ne a yau 10 ga Yuni 2019, bayan bincikin na'ura ya gano wata rumfa a Alafa cikin dajin Sambisa inda yan ta'addan ke amfani da shi wajen baiwa maharansu umurni."

Yayinda jirgin ya gano gidan daga sama, ya hangoshi cike da yan ta'addan a cikin. Ba tare da bata lokaci ya sakar musu wutar aradu wanda ya ragargaza cibiyar tare da kisan yan ta'addan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel