Babu ruwan Oyegun wajen matsalar da APC ta shiga – Erhahon

Babu ruwan Oyegun wajen matsalar da APC ta shiga – Erhahon

Mun samu labari cewa tsohon Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC, Kwamared Godwin Erhahon ya fito ya kare John Odigie-Oyegun, wanda ake zargi da jefa jam’iyyar cikin matsala.

Godwin Erhahon ya bayyana cewa bai dace a rika daura nauyin cikas din da APC ta fuskanta a kan tsohon shugaban jam’iyyar na kasa ba. Erhahon yace daurawa John Odigie-Oyegun alhaki, sam bai da wani amfani.

Erhahon yace masu wannan kokari na bata John Oyegun, za su kara jefa Kwamared Adams Oshiomhole cikin sarkakiya ne, a yayin da su ke kokarin dauke duk wani nauyin matsalar da aka samu a 2019 daga wuyansa.

A cewar sa:

“Yunkurin ganin laifin John Oyegun game da abubuwan da su ka faru ga jam’iyyar APC, ya jawo bakin jini da kuma fushi a kan jagorancin jam’iyyar da ke kai a yanzu.”

KU KARANTA: Gwamnonin APC sun yi wani zama na musamman a Abuja

Ya ce:

“Adams Oshiomhole wanda ya fito daga Yankin Arewacin jihar Edo, da kuma tsohon yaronsa watau gwamna mai-ci a yau, Godwin Obaseki, ba a ga maciji a yanzu, don haka babu hikima wajen jefa Oyegun cikin wannan rikici.”

“Har wa yau, kiran da wasu Magoya bayan Gwamna Obaseki su ke yi na Adams Oshiomhole ya sauka daga kujerar shugaban Jam’iyya…

Jawabin na sa ya ce:

“…Wannan ya sake jefa Gwamnan (na Edo) cikin matsala a daidai lokacin da yake kokarin musanya cewa an samu wani sabani tsakanin sa da Maigidansa (Adams Oshiomhole).

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel