Yaki da cin hanci: Buhari ya karbi bakuncin kwararru daga kasar Italiya (Hotuna)

Yaki da cin hanci: Buhari ya karbi bakuncin kwararru daga kasar Italiya (Hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wasu wakilan gwamnatin kasar Italiya da zasu taimaka wa Najeriya kwato kadarori da dukiyoyin da 'yan kasar suka saya da kudaden cin hanci a kasashen ketare.

A sanarwar da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa ya fitar, ya ce Buhari ya yi maraba da yunkurin gwamnatin kasar ta Italiya na taimakon Najeriya a yakin da take yi da cin hanci da karya tattalin arzikin kasa.

Wani dan Najeriya da ya kasance bakin mutum na farko da ya taba cin zaben dan majalisa a kasar Italiya na daga cikin tawagar wakilan da suka ziyarci Buhari, kuma zai zauna a gida Najeriya domin halartar bukukuwan bikin zagayowar ranar dimokraddiya, 12 ga watan Yuni, wanda za a yi ranar Laraba.

Kazalika, ya taya shugaba Buhari murnar sake samun nasarar lashe zaben kujerar shugaban kasa a karo na biyu, kamar yadda Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Yaki da cin hanci: Buhari ya karbi bakuncin kwararru daga kasar Italiya (Hotuna)

Buhari ya karbi bakuncin kwararru daga kasar Italiya
Source: Facebook

Yaki da cin hanci: Buhari ya karbi bakuncin kwararru daga kasar Italiya (Hotuna)

Buhari ya karbi bakuncin kwararru daga kasar Italiya
Source: Facebook

Yaki da cin hanci: Buhari ya karbi bakuncin kwararru daga kasar Italiya (Hotuna)

Wakilan gwamnatin kasar Italiya da Buhari
Source: Twitter

Yaki da cin hanci da karya tattalin arzikin kasa na daga cikin manufofin gwamnatin shugaba Buhari.

Gwamnatin Buhari ta kwace kadarori masu yawa daga hannun tsofin shugabanni da ma'aikatan gwamnati da ake tuhuma da cin hanci.

DUBA WANNAN: Abinda yasa na gudu na bar gidan miji na - Matar tsohon gwamna a PDP

Kazalika, ta aika wasu tsofin gwamnoni da shugabannin hukumomin da aka samu da laifin wawure kudin kasa zuwa gidan yari.

A kwanakin baya ne shugaba Buhari ya bawa ministar kudinumarni ta hada kai da hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) domin sayar da dukkan kadarorin da akwa kwace daga hannun wadanda aka gurfanar a kotu bisa tuhumar su da cin hanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel