Yanzu-yanzu: Buhari ya rattaba hannu kan dokar ranan tunawa da Abiola

Yanzu-yanzu: Buhari ya rattaba hannu kan dokar ranan tunawa da Abiola

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar mayar da ranar 12 ga watan Yuni na kowani shekara matsayin sabuwar ranar Demokradiyya sabanin 29 ga Mayu da ake yi tun shekarar 1999.

A shekarar 2018, shugaba Buhari ya alanta 12 ga Yuni matsayin ranar Demokradiyya ne domin tunawa da gwagwarmayan da ya faru a shekarar 1993 da kuma karrama marigayi Cif MKO Abiola wanda ya lashe zaben shugaban kasan 1993.

A ranar Talata, 12 ga watan Yuni 2019 za'a yi murnan sabuwar ranar Demokradiyya a fadin Najeriya kuma gwamnatin shugaba Buhari ta sanarwa jama'a cewa babu aiki. Ana kyautata zaton cewa Buhari zai gabatar da jawabin da ya kamata ace ya gabatar a ranar 29 ga Mayu.

KU KARANTA: Babu ma'alukin da zai iya hana Buhari sake nada ni minista - Solomon Dalung

A rana irinta, 12 ga watan Yuni, 1993, marigayi Cif Moshood Abiola ya tsaya takarar zaben kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Social Democratic Party SDP inda ya lallasa abokin hamayyarsa, Alhaji Bashir Tofa.

Yayinda ake sanar da sakamakon zaben kuma ya bayyana cewa Abiola zai lashe zaben, sai shugaban kasan mulkin soja a lokacin, Janar Ibrahim Babangida, ya bada umurnin dakatad da sanar da sakamakon. Daga bisani ya sanar da cewa an yi watsi da zaben gaba daya.

Tun daga lokacin Cif MKO Abiola ya fara gwagwarmayan kwato hakkinsa wanda hakan ya sa aka daureshi har ya rasa rayuwarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel