Babu wanda zai hana mu binciken Sarki Sanusi, inji Hukumar yaki da cin hanci ta Kano

Babu wanda zai hana mu binciken Sarki Sanusi, inji Hukumar yaki da cin hanci ta Kano

-Hukumar yaki da cin hanci a jihar Kano ta lashi takobin cigaba da binciken Sarkin Kano bisa zarginsa da ake da almundahanar wasu kudade na masarautar Kano.

-Muhyi Magaji shugaban hukumar ne ya bayyana wannan aniya tasu ga manema labarai, inda yake cewa hukumarsu zaman kanta takeyi.

Hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta ce maganar binciken Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II kan zarginsa da almundahanar wasu kudade mallakar masarautar na nan daram duk da cewa ya yi sulhu da Ganduje.

Hukumar ta ce: “ Muna aiki ne a matsayinmu na hukuma mai zaman kanta bisa la’akari da abinda ya bayyana gabanmu daga wasu dake da kusanci da masarautar tun ranar 28 ga watan Maris, 2017.”

KU KARANTA:Da alamu Boss Mustapha da Abba Kyari su cigaba da rike mukamansu

Har wa yau, hukumar ta cigaba da cewa: “ Masu karar na zargin Sarki Sanusi da kashe wasu kudade na masarautar ba bisa ka’ida ba.”

Barista Muhyi Magaji, shugaban hukumar ya ce: “ mun fara gudanar da bincike kan wannan tuhumar da akeyi wa Sarki tun lokacin da muka samu wannan korafi kamar yadda dokar aikinmu ta bamu dama.”

Shugaban ya cigaba da cewa: “ mun fuskanci wadansu matsaloli a daidai lokacin da muka fara gudanar da binciken namu. Daya daga ciki shi ne yinkurin gwamnati da take domin tsige sarkin da duk wanda keda sa hannu cikin lamarin, kamar yadda wasu ke fadi.”

Haka zalika shugaban ya sake cewa: “ wannan binciken namu bai da dangantaka ta nesa ko ta kusa da gwamnatin Kano, sai dai kawai saboda korafin jama’a wadanda suka kawo mana kara . Idan baku manta ba hukumarmu zaman kanta ta keyi ba wasu muke yi wa aiki ba.”

“ Mun kawai nemi izinin gwamnati ne a hukumance domin bin tsarin yadda aikinmu ya tanada. Ko shakka babu hukumarmu zata cigaba da bin wannan badakkala har sai gaskiya ta bayyana.” A cewar Muhyi.

Barista Muhyi Magaji ya ce:"Duba ga yaki da cin hanci da gwamnatin Najeriya keyi a yanzu, hukumar nada yaqinin cewa duk wanda aka samu da laifin rashawa ba zai sha ba ko da kuwa wane ne shi."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel