Sunaye: Rundunar soji ta kashe mutane 9 dake yada labaran kungiyar Boko Haram

Sunaye: Rundunar soji ta kashe mutane 9 dake yada labaran kungiyar Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe mutane 9 dake watsa labaran kungiyar Boko Haram, wacce da ta rikide zuwa ISWAP, a kafafen sadarwa da dandalin sada zumunta.

Sagir Musa, darektan yada labarai da hulda da jama'a na rundunar sojin Najeriya, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce kashe 'yan kungiyar sadarwa na kungiyar Boko Haram ya tabbatar da cewar rundunar soji ta gama gurgunta dukkan aiyukan kungiyar.

Ya lisafa sunayen mutane 9 da aka kashe kamar haka: Abu Hurayra al-Barnawi, Ali alGhalam al-Kajiri, Abu Musab Muhammed Mustafa al-Maiduguri, Abu Abdullah Ali al-Barnawi, da Abu Musa al-Camerooni.

Ragowar sune; Ahmed al-Muhajir, Abu Ali al-Bamawi, Abu Khubayb bin Ahmed al-Barnawi da Abu al-Qa'qa' al-Maiduguri.

"Kowa ya san kungiyar na amfani da kafafen yada labarai domin yada farfaganda a kokarinta na kafa daular mulki irin nata," a cewar sa.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi magana a kan kisan mutane 25 a jihhar Sokoto

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar tun a shekarar 2009 kungiyar Boko Haram ta fara amfani da kafafen sadarwa, musamman a dandalin sada zumunta, domin yada faifan bidiyo da lakcoci domin jan hankalin matasa daga kasashen Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi su shiga kungiyar.

NAN ta kara da cewa kungiyar ta canja salo a shekarar 2014 ta hanyar bude shafuka da dama a dandalin sada zumunta irin su 'Facebook' da Tuwita domin isar da sakonni da kuma tuntubar jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel